27 Oktoba 2020 - 11:13
​Najeriya: An Cafke Daruruwan Masu Wasoson Ganima A Rumbunan Ajiye Abinci

An kame daruruwan mutane a wasu jihohin Najeriya sakamakon samunsu a cikin wadanda suka shiga fasa rumbunan ajiyar kayan abinci da shaguna suna kwasar ganima.

ABNA24 : Gidan rediyon Faransa ya bayar da rahoton cewa, jama’a da dama a wasu jihohin Najeriya sun yi fitar dango suna farfasa duk inda suke tsammanin an boye kayayyakin abinci da na masarufi suna wasoso, kuma sun shafe ilahirin karshen makon da ya gabata suna cin karensu babu babbaka.

Wadannan mutane dai sun hada ne da mata da maza, matasa har ma da magidanta, wasu ma rike da ‘ya'yansu, wadanda suka yi amannar cewa kayyakin abincin da aka bayar a raba musu ne aka boye, kuma suke rage wa hukumomi aiki wajen dibar abin da suka kira nasu.

Rahotanni sun ce bayan Lagos da Osun da aka fara samun matsalar, an kuma samu a Jihohin Edo da Anambra da Kaduna da Plateau da Cross Rivers da Ekiti, baya ga Adamawa da Abuja babban birnin Najeriyar.

Tuni rundunar ‘yan sandan Najeriya ta umurci jami’anta da su shiga farautar masu fakewa da zanga zangar EndSARS suna fasa rumbunan ajiyar gwamnati da na daidaikun mutane.

Ya zuwa yanzu rahotanni sun ce kusan mutane dari 5 da ake zargi sun aikata wannan aika aika ne suka shiga hannun ‘yan sanda a jihohin Lagos, Akwa Ibom, Osun, Anambra, Kano da Filato.

342/