ABNA24 : Wannan dai na zuwa ne ganin yadda 'yan Jam’iyyar Democrat suka mayar da hankali ka’in da na’in wajen yakin neman zabe, a lokaci guda kuma suna samun goyon bayan jama’ar Amurka fiye da Donald Trump, wanda hakan ke nuni da cewa mai yiwuwa ya sha kayi a zaben.
Manyan sanatocin na jam’iyyar Trump ta Republican suna yin hakan ne domin kare kujerunsu a zabuka masu zuwa, domin kada su ma su sha kayin da suke zaton cewa Trump zai sha a zaben, inda suka fara sukarsa da salon siyasarsa a bainar jama’a, sabanin lokutan baya da suke kumfan baki wajen kare shi da kuma salon siyasar tasa.
Donald Trump wanda ba shi da wata gogewa kan lamurra da suka shafi siyasa, ya tsaya takarar shugabancin kasar Amurka kasantuwarsa shi hamshakin mai kudi ne, ya kuma yi amfani da kudinsa wajen nema ma kansa kujerar shugabancin kasar,
342/