12 Oktoba 2020 - 15:24
Jihadi Islami Ta Ja Kunnen ‘Isra’ila’ Dangane Da Halin Da Fursunoni Palastinawa Suke Ciki

Rundunar Quds Brigade, bangaren soji na kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Jihadi Islami ta Falastinu ta ja kunnen haramtacciyar kasar Isra’ila dangane da halin da fursunoni Falastinawa suke ciki a gidajen yarin haramtacciyar kasar.

ABNA24 : Rundunar ta bayyana hakan ne cikin wan faifan bidiyo da ta fitar mai suna ‘Hakurin Mu Na Da Iyaka’ ta nuna babban sakataren kungiyar ta Jihadi Islami Ziyad Nakhalah yana jan kunnen sahyoniyawan dangane da mummunan halin da fursunonin suke ciki musamman Maher Al-Akhras, daya daga cikin fursunonin da ya shafe sama da watanni biyu yana yajin cin abinci.

A cikin faifan bidiyon dai, rundunar Quds Brigade din sun nuna wasu makamansu masu linzami inda suka yi barazanar cewa matukar wani abu ya sami Maher Al-Akhras din to kuwa ba za su yi shiru ba.

A ranar Juma’ar da ta gabata ce kwamitin kula da fursunoni Falastinawa da suke tsare a gidajen yarin HKI ya fitar da wani rahoto da ke nuni da irin halin ko in kula da mahukuntan HKI suke nunawa dangane da mummunan yanayin da fursunoni Falastinawan suke ciki.

342/