ABNA24 : Da yake sanar dahakan babban sakataren MDDr, Antonio Guteress, Ya bayyana cewa ana matukar bukatar kudade a halin yanzu domin kada a rasa damar da ake da ita ta samar da riga-kafin cutar.
Mista Guteress Ya kara da cewa, hadin kan kasashe wurin nemo riga-kafin cutar ne kawai zai taimaki duniya baki daya.
Kiran da Mista Guterres ya yi na zuwa ne bayan da shugaban kungiyar samar da riga-kafi ta duniya, Seth Berkley, ya yi kira ga kasashe su bayar da taimako.
Ana dai bukatar dala biliyan biyu zuwa watan Disamba domin samar da riga-kafin cutar ga kasashe 92 masu tasowa, inji shugaban kungiyar samar da riga-kafi ta duniya.
342/