29 Satumba 2020 - 12:20
MDD Ta Yabawa Ci Gaban Da Bangarorin Libiya Suka Samu

Ofishin tawagar MDD dake kasar Libiya (UNSMIL), ya yabawa irin nasarorin da aka cimma da irin halayyar da wakilan bangarorin kasar Libiya suka nuna a yayin tattaunawar tsaro da al'amuran sojoji da aka gudanar a Masar.

ABNA24 : Sanarwar da tawagar (UNSMIL) ta fitar ta ce, tawagar sojoji da 'yan sanda daga gabashi da yammacin Libiya sun fara taron tattaunawar tsaro da al'amurran soji, karkashin yarjejeniyar tattaunawar hadin gwiwar sojoji ta 5+5 Joint Military Commission.

UNSMIL ta mika sakon godiya ga gwamnatin Masar sakamakon shirya muhimmiyar tattaunawar, Kana ta yabawa wakilan bangarorin biyu bisa yadda suka nuna halayyar sanin ya kamata a tattaunawar wacce aka shirya da nufin kawo karshen tashe tashen hankula a tsakiyar Libiyar.

Ofishin MDDr dake Libiya yana fatan sakamakon da za a samu a tattaunawar ta gaba da gaba, zai kasance a matsayin share fagen shiga hakikanin tattaunawar hadin gwiwar 5+5.

342/