23 Satumba 2020 - 10:14
Iran : Rauhani Ya Yi Jawabi A Taron MDD Karo Na 75

Shugaban kasar Iran, Hassan Rohani, ya gabatar da jawabinsa a taron MDD, karo na 75.

ABNA24 : A cikin jawabinsa shugaba Rauhani, ya tabo batutuwa da dama da suka shafi siyasar kasa da kasa dama halin da duniya ke ciki.

Batun Falasdinawa dake ci gaba da fuskantar zaluncin mahukuntan yahudawan Isra’ila.

A hannu daya kuma shugaba Rauhanin, ya bayyana Shahid, Qassim Sulaimani a matsayin wanda ya sadaukar da rayuwarsa ga dukkan bangarorin al’ummar yankin musulmi da Kristocinsu daga barazanar kungiyar Da’esh.

Dakta Rauhani, ya kuma godewa MDD, da kasashen China da kuma Rasha, kan matakinsu na hawa kujerar na ki game da wasu kudurorin Amurka kan kasarsa.

Iran ba zata taba canza siyasarta ko manufofinta ba ta hanyar mika kai.

342/