20 Satumba 2020 - 12:47
Siriya : MDD Ta Gargadi Turkiyya Kan Take Hakkin Dan Adam

MDD ta bukaci gwamnatin kasar Turkiya ta gabatar da bincike mai zaman kansa dangane da rahotannin take hakkin bil’adana wanda sojojinta da kuma kungiyoyin da suke samun goyon bayanta suke aikatawa a arewacin kasar Siriya.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya nakalto babban kwamishina mai kula da kare hakkin bil’adana na majalisar ya na fadar haka a safiyar yau Asabar a birnbin Geneva.

Michelle Bachelet, ya bayyana cewa akwai rahotannin sace-sacen mutane, da kissan wasu da kuma aikata laifuffukan yaki a yankunan arewacin kasar Siriya wadanda suke karkashin ikon gwamnatin kasar ta Turkiyya.

Shugaban hukumar (OHCHR) ya ce sun fara samun hotuna, wadanda suke tabbatar da an aikata irin wadannan laifuffuka a wadannan yankunan.

342/