19 Satumba 2020 - 11:04
Libya:Haftar Ya Yi Alkawarin Dage Hanin Sayar Da Danyanen Man Fetur Na Kasar Amma Tare Da Sharadi

Kwamandon sojojin gabacin kasar Libya Halifa Haftar ya bada sanarwan cewa, zai amince ya dage hanin sayar da danyen man fetur na kasar wanda ya kai watannin 8 ya na aiwatarwa, amma tare da sharadin za’a yi rabon adalci a kudaden da aka samu.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto Khalifa Haftar ya na fadar haka a jiya Jumma’a, ya kuma kara da cewa zai dage hanin saida danyen man din na wata guda, sannan ya ga irin rabon da za’a yi.

Labarin ya kara da cewa wannan shi ne sassaunci na farko wanda shgaban sojojin gabacin Libya ya yi, tun bayan ya kasa samun nasara a kan gwamnatin Tripoli watanni 14 da suka gabata.

Kafin haka dai kasar Libya ta na saida ganga miliyon 1.2 na danyen man fetur a ko wace rana, idan an kwatanta da gangan 100,000 kacal da ake haka a ahalin yanzu.

Kasar Libya dai ta fada cikin rigingimun cikin gida tun bayan kifar da gwamnatin Mu’ammar Kazzafi a shekara ta 2011.

342/