17 Satumba 2020 - 09:59
​Venezuela Ta Kakkabo Jirgin Saman Amurka A Sararin Samaniyar Kasar

Gwamnatin kasar Venezuela ta bada sanarwan cewa sojojin kare sararin samaniyar kasar sun kakkabo wani jirgin sama mallakin gwamnatin kasar Amurka dauke da miyagun kyayoyi wanda ya ratsa ta sararin samaniyar kasar kusa da kan iyakar kasar da kasar Colombia.

ABNA24 : Tashar talabijin ta Hispantv ta nakalto ministan cikin gida na kasar ta Venezuela Néstor Reverol yana fadar haka.

Ya kuma kara da cewa sojojin kasar a shirye suke su kare sararin samaniyar kasar a duk lokacinda makiya suka yi kokarin keta hurumin sa.

Dangantaka tsakanin Amurka da Venezuela ta yi tsami ne tun shekara ta 2018 a lokacinda aka gudanar da zaben shugaban kasa, wanda kuma shugaba Nicols Madoro ya lashe.

Amma Amurka ta ki amincewada sakamakon zaben sannan ta dorawa kasar Takunkuman tattalin arziki masu tsanani don kifar da gwamnatin kasar.

342/