16 Satumba 2020 - 15:26
​Washington: Bahrain Da UAE Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejejniyar Kulla Alaka Da Isra’ila

Gwamnatocin kasashen Bahrain da hadaddiyar daular larabawa sun rattaba hannu tare da firayi ministan Isra’ila kan kulla alaka da gwamnatin yahudawan Isra’ila a fadar White House da ke birnin Washington na Amurka.

ABNA24 : Tashar RT ta bayar da rahoton cewa, dukkanin bangarorin uku sun rattaba hannu a kan abin da suka kira yarjejeniyar zaman lafiya a tsakaninsu, inda suka jaddada cewa za su ci gaba da yin aiki tare a tsakaninsu.

Gwamnatin Amurka ce dai ta jagoranci rattaba hannu kan wannan yarjejeniya, inda shugaban kasar Amurka Donald Trump ne ya jagoranci taron rattaba hannun, wanda kuma ya bayyana cewa kafin taron ya tattauna da sarkin Saudiyya Salman bin Abdulaziz da kuma yarimansa Muhammad Bin Salman ta wayar tarho, kuma sun nuna goyon bayansu kan hakan, kuma su ma za su biyo baya.

Trump ya ce ya bayar da umarnin a yanke duk wani tallafi da Amurka take baiwa Falastinawa, saboda ba su girmama gwamnatin Amurka.

342/