ABNA24 : Kungiyar ta ce ‘’halin da ake ciki a kasar Yemen, dake fama da yaki na tsawon shekaru shida na da matukar daukan hankali, duba da matsalolin da ake fuskanta wajen shiga da kayan agaji.
A rahoton data fitar kungiyar ta HRW, ta ce babban abun damuwa shi ne tsauraren matakai da bangarorin dake rikici da juna a kasar suka gindaya kafin raba tallafin.
Tun a bara ne kungiyoyin MDD da masu zaman kansu ke kokarin samun izinin shiga kasar saidai hakan ya cutura sakamakon tsauraren sharudan da bangarorin ke gindayawa kafin su amince da tallafin.
Wata matsalar kuma ita ce yadda bangarorin ke karkata tallafin ga masu goyan bayansu.
MDD, dai ta bayyana halin da Yemen ke ciki a matsayin bala’I mafi muni a duniya, inda kashi 80 cikin dari na al’ummar kasar ta Yemen ke dogaro da tallafi.
Ko baya ga hakan yakin da kasar ke fama da shi ya yi sanadin mutuwar gomman dubban mutane da kuma tilasta wa wasu miliyan uku kauracewa muhallansu.
342/