13 Satumba 2020 - 11:59
Zanga zangar Kin Jinin Netanyahu Na Ci Gaba Da Yaduwa A Isra’ila

A Isra’ila dubban jama’a ne suka sake fitowa a zanga zangar kin jinin fira ministan Isra’ilar Benjamin Netanyahu, wanda ake tuhuma da cin hanci da rashawa da kuma gazawa wajen shawo kan annobar korona da kuma tasirin data haifar kan tattalin arziki.

ABNA24 : Bayanai sun ce duk da halin da ake ciki na fama da annobar korona dubban mutane suka fito zanga zanga da yammcin jiya Asabar a cikin manyan birane domin kira ga fira ministan Netanyahun ya yi murabus.

Rahotanni sun ce a birnin Qudus dubban masu zanga zange ne sukayi tattaki akan tutuna kafin daga bisani su isa gidan firaministan.

A watan Nowamba 2019, aka tuhumi Netanyahu da cin hanci da rashawa da cin amana da kuma zamba, wanda shi ne karon a tarihin Israilar da ake tuhumar fira minista da aikata wadanan laifuka a cikin wa’adinsa.

Trump Ya Sanar Da Kulla Alaka Tsakanin Bahrain Da Gwamnatin Yahudawan Isra’ila

A watannin baya baya nan, yawan marasa aiki a Isra’ila ya haura kaso 20% sabanin 2,4% a watan Fabarairu, sannan yawan masu kamuwa da cutar korona shi ma ya karu inda yanzu mutane 152,525 suka kamu da cutar sai kuma 1,101 da suka mutu, wanda ake bayyana shi a matsayin adadin mafi muni idan akayi la’akari da yawan jama’ar da Isra’ilar take da shi na miliyan tara.

342/