11 Satumba 2020 - 13:13
Lebanon : An Sake Samun Gobara A Tashar Ruwan Beirut

A Lebanon, wata gobara ta sake tashi a tashar ruwan Beirut, wata guda bayan wacce ta tashi ta hadassa mummunar fashewa wacce ta yi sanadin muturwar mutane 192 da kuma jikkata sama da 6500.

ABNA24 : Rahotanni daga kasar sun ce an samu wata babbar gobara data tashi ranar Alhamis din nan a tashar ruwan ta Beirut.

Babu dai karin bayyani kan musababin tashin gobarar wacce ta tashi a wuraren ajiye kayayaki na bangaren tashar ruwan da ya fuskanci mummunar barna a ranar 4 ga watan Agusrta da ya gabata.

Bayanai sun ce hankali jama’a ya tashi sosai lokacin da gobarar ta tashi.

Tuni dai sojoji suka bukaci ma’aikata da jama’a dasu fice daga wajen, yayin da ‘yan jami’an kwana kwana ke kokarin kashe gobarar.

342/