7 Satumba 2020 - 12:04
Gambia Ta Fusata Da Takunkumin Da Amurka Ta Sanyawa Jami'an ICC

Gwamnatin kasar Gambia ta bayyana rashin jin dadinta bisa matakin da gwamnatin Amurka ta dauka na kakaba wa wasu manyan jami'an kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa su guda biyu.

ABNA24 : Amurka ta sanya takunkumi kan babbar mai gabatar da kara ta kotun ICC Fatou Bensouda, wacce ‘yar asalin kasar Gambia ce, da kuma wani babban jami'in kotun.

A cewar gwamnatin Gambiya, wannan mataki na Amurka mummunan saba doka ne, kuma yunkuri ne na kawo cikas ga muhimman ayyukan kotun ta ICC a musamman yakin da take yi wa masu aikata manyan laifuka a kasa da kasa.

Ita dai Amurka ta dau matakin ne a matsayin mayar da martani game da tuhumar da kotun ta ICC ke yi wa wasu sojojin Amurka na aikata laifukan yaki a Afghanistan.

342/