ABNA24 : Shugaban gamayyar kungiyar ‘yan tawaye ta Sudan Alhaji Idris ya bayyana cewa; “Wannan shi ne lokacin farko da aka yi ganawa a tsakanin bangarorin biyu tun bayan rattaba hannu akan yarjejeniyar sulhun.”
Shi kuwa shugaban kungiyar ‘yan tawaye ta yankin Darfur Minni Minawi ya bayyana cewa; Muhimman abubuwan da suke gabanmu su ne bunkasa tattalin arziki da ayyukan jin kai ga mutanen da suke a daidaice.
Gamayyar kungiyar ‘yan tawayen ta Sudan ta kunshi mayakan yankunan Darfur, da Kurdufan ta kudu da arewa da kuma Blue Nile.
342/