ABNA24 : Wasu daga cikin mutanen Burundi sun dauki matakin tserewa daga muhallinsu ne domin gujewa shiga cikin rikici tun bayan da Shugaban kasar a wancan lokaci Pierre Nkurunziza ya dauki matakin yin tazarce a kan karagar mulkin kasar a wa’adi na uku bayan kare wa’adi biyun da kundin tsarin mulkin kasar ta kayyade masa a kokarin da ya yi na gudanar da kwaskwarima a kundin tsarin mulkin kasar lamarin da ya janyo rikicin siyasa da tashe-tashen hankula da ya suka janyo hasarar rayukan daruruwan mutane.
Ministan harkokin cikin gidan kasar Burundi a halin yanzu Gervais Ndirakobuca yana bayyana cewa: Wannan wani yunkuri ne mai cike da tarihi, don haka muna tsananin farin cikin ganin al’ummarmu sun dawo gida cikin aminci dauke da kyakkyawar fata bayan shafe tsawon shekaru suna gudun hijira nesa da kasarsu.
Sabon shugaban kasar Burundi Evariste Ndayishimiye ya lashe zaben shugabancin kasar ne tun a watan Yuni, inda ya yi kira ga dukkanin ‘yan kasar da suke gudun hijira su dawo gida domin sake gina wata sabuwar al’umma a Burundi.
342/