ABNA24 : Kafofin yada labaran kasar Syria sun bayar da rahoton cewa, a yau ne Faleh Fayyad ya isa birnin Damascus dauke da sakon wasika daga firayi ministan Iraki Mustafa Kazimi, zuwa ga shugaba Assad na Syria.
Shuga Assad ya tarbi Fayyad a fadarsa da ke birnin Damascus, inda ya karbi sakon wasikar, baya ga haka kuma sun tattauna a kan batutuwa daban-daban dangane da sakon na Kazimi.
Firayi ministan Iraki dai ya sheda wa Assad a cikin wasikar cewa, ya zama wajibi kasashen Iraki da Syria su kara hada karfi da karfe domin yin aiki tare a dukkanin bangarori, musamman a batun tsaro, da kuma tunkarar barazanar ‘yan ta’adda da suka addabi kasashen biyu.
Kazimi ya ce dole ne sojojin Syria da Iraki su yi aiki tare domin tunkrar duk wata barazana a kan kasashensu, kamar yadda kuma dole ne su karfafa harkoki na tattalin arziki da cinikayya a tsakanin kasashensu.
Shugaba Assad na Syria ya bayyana farin cikinsa matuka dangane da wannan matsay ata gwamnatin Iraki, tare da bayyana shirin Syria na yin aiki tare da gwamnatin Iraki a dukkanin bangarori.
342/