ABNA24 : Bugu da kari al-Sirraj ya zargi madugun yaki Janar Halifa Haftar da yi wa shirin zaman lafiya kafar angulu.
A jawabin da ya gabatar a jiya Lititin, shugaban gwamnatin kasar ta Libya, Fayez al-Sirraj ya ce, al’ummar kasar suna da hakkin yin Zanga-zanga, kuma wajibi ne ga gwamnatinsa ta saurari kokensu da kuma biya musu bukatunsu.
A gefe daya shugaban gwamnatin hadin gwiwar kasar ta Libya al-Sirraj ya kuma dora alhakin yi wa shirin kawo karshen yaki kafar angulu akan janar Halifa Haftar. Har ila yau, ya ce; Wanda ya kallafawa al’ummar kasar Libya yaki na tsawon watanni 14 ya nace akan ci gaba da yakin sannan kuma da hana su cin moriyar albarkatu man fetur din kasar.
342/