16 Agusta 2020 - 10:37
Iraqi: An Kama Manya-Manyan Mayakan Daesh A Arewacin Kasar

Ma’aikatar cikin gida ta kasar Iraqi ta bada sanarwan kama wasu manya-manyan mayakan kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh a lardin Ninawa daga arewacin kasar.

ABNA24 : Shafin yanar gizo na “Ra’ayul Yaum” ya nakalto ma’aikatar ta na fadar haka a yau Asabar . Ta kuma kara da cewa bayan kama Ibn Ingimasi, wanda akewa lakabi da Abu-Khattab ya tabbatar da cewa ya na daga cikin kwamitin kafa dokoki na gwamnatin Daesh da ta rushe.

Har’ila yau an kama wasu mutane biyu tare da shi wadanda su ma suna daga cikin wadanda suke da babban matsayi a gwamnatin ta Daesh.

Mutanen ukku sun tabbatar da cewa suna da hannu a cikin hare-hare da dama wadanda kungiyar ta kai kan jami’an tsaro da kuma mutanen kasar ta Iraqi.

An kawo karshen gwamnatin Daesh a kasar Iraqi tun shekara ta 2017, amma har yanzun akwai ‘ya’yan kungiyar wadanda a boye suke shirin sake yunkurowa.

Labarin ya kammala da cewa a cikin watannin biyu da suka gabata wato Mayu da Yuni, jami’an tsaron kasar Iraqi sun kama mayakan Daesh 419.

342/