ABNA24 : taya al-ummar kasar Lebanon musamman gamayyar masu gwagwarmaya dangane da cika
shekaru 14 da nasarar da kungiyar Hizbullah ta samu kan sojojin HKI a yakin
kwanaki 33 a shekara ta 2006.
Tashar talabijin ta Almasirah ta kasar Yemen ta nakalto kakakin kungiyar ta Ansarullah Mohammad Abdussalam yana cewa, wannan rana ta nasara ta bana ta na zuwa ne a dai-dai lokacin munafukan kasashen Larabawa suka bayyana amincewarsu da gwamnatin HKI.
An fara yakin kwanaki 33 tsakanin sojojin kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon da na yahudawan a cikin watan Yulin shekara ta 2006 sannan aka kareshi a rana irin ta yau wato 14 ga watan Augustan shekara ta 2006. Inda kungiyar Hizbullah ta sami gagarumin nasara kan sojojin yahudawan sahyoniyya. Su kuma suka janye daga kasar Lebanon a kaskance.
342/