12 Agusta 2020 - 10:10
Nijar: 'Yan Boko Haram Na Ci Gaba Da Garkuwa Da Mutane A Diffa

Boko Haram tana Ci Gaba Da Yin Garkuwa Da Mutane

ABNA24 : Boko haram tana ci gaba da sace mutane tana yin garkuwa da ku, inda a cikin wannan makon kawai ta yi awon gaba da mutane 20.

Tare da cewa da akwai dokar ta-baci a cikin yankin da kuma hana kai da komaowa da aka kakaba tun 2015, satar mutane domin yin garkuwa da su da a wasu lokutan ake neman kudaden fansa, ko kuma yi musu kisan gilla yana nuni da cewa matsalar tsaro ta ta’azzara a cikin yankin.

A cikin daren juma’a, 7 ga watan Agusta 2020, ‘yan bindiga sun yi awon gaba da wasu mutane a cikin yankin na Diffa, wadanda ake kyautata zaton cewa ‘yan Boko Haram ne. Mutanen yankin sun sanar da cewa, mnutane da aka sace din sun hada da mata a kauyen Jakimea.

A can garin Kolo Manga ma an sace wasu mutanen 4. Sai kuma ranar Laraba da aka yi awon gaba da wasu mutane 14 da su ka hada da jarirai 2.

Kungiyar Boko Haram ta zama babbar barazana ta tsaro ga kasashen da su ka hada Nijar, Nijeriya, kamaru da kuma Chadi.

342/