11 Agusta 2020 - 10:17
​Musawi: Wasu Na Amfani Da Hatsarin Da Ya Auku A Lebanon Domin Cimma Manufofinsu Na Siyasa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Sayyid Abbas Musawi ya bayyana cewa, wasu bangarori da wasu kasashe suna yin amfani da hatsarin da ya auku a kasar Lebanon, domin cimma burinsu na siyasa a kasar.

ABNA24 : A lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai yau a birnin Tehran, Musawi ya bayyana cewa; al’ummar kasar Lebanon a halin yanzu suna bukatar natsuwa da kwanciyar hankali, domin kuwa hatsarin da ya faru ya shafi kasar ne baki daya, kuma abu ne da yake bukatar bincike domin gano hakikanin lamarin da ya faru, kuma abin da ake ciki kenan.

Ya ce wasu bangarori a kasar da ma wasu kasashen ketare, sun dauki hakan a matsayin wata babbar dama ta cimma burinsu na siyasa a kan kasar ta hanyoyi daban-daban, wanda kuma hakan ko kadan babu ta inda zai amfanar da al’ummar Lebanon, sai kara jefa su cikin mawuyacin hali, wanda kuma ya kamata al’ummar kasar su zama cikin fadaka dangane da hakan.

Dangane da wasikar da sakataren majalisar kasashen larabawan yankintekun fasha ya aike wa kwamtin tsaron majalisar dinkin duniya domin neman a kara tsawaita takunkumin hana Iran saye da sayar da makamai kuwa, Musawi ya bayyana cewa, kasashen da suka aike da wasikar, su ne suka cika yankin gabas ta tsakiya da muggan makamai na daruruwan biliyoyin daloli da suke saye daga Amurka da kasashen turai, saboda haka su ne ya kamata a dora wa ayar tambaya kan manufarsu.

342/