5 Agusta 2020 - 12:26
Lebanon : Adadin Wadanda Suka Rasu A Tagwayen Fashe fashe Ya Haura Mutum 100

A Lebonon adadin mutanen da suka rasa rayukansu a jerin fashewar data auku a tashar ruwan Beirut, ya haura mutum 100 a cewar kungiyar agaji ta kasar.

ABNA24 : A wata sanarwa data fitar kungiyar ta ce har yanzu ana ci gaba da aikin ceto a wurin da kuma gewayen inda lamarain ya faru.

Kawo yanzu kuma adadin wadanda suka jikkata sanadin fashewar ta jiya sun kai sama da mutum 4,000 a cewar kungiyar.

Bayanan farko farko sun nuna cewa fashewar na da nasaba ne da wasu sinadarai sama da ton 2,750 da aka ajiye a wani wajen ajiye kayayyaki na tsawon shekaru shida, suka janwo wannan barna.

Tuni dai aka fara zaman makoki na kwanaki uku domin juyayin wannan iftila’in.

Lamarin dai ya girgiza al’ummar kasar ta Lebanon kwarai da gaske, a daidai lokacin da kasar ke fama da matsin tattalin arziki da kuma annobar korona.

342/