3 Agusta 2020 - 13:41
​Netanyahu Ya Zargi Kafofin Yada Labaran Isra’ila Da Tunzura Masu Zanga-Zanga A Kansa

Firai Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya dirar mikiya kan kafofin yada labaran Isra’ila, tare da zarginsu da cewa su ne suke tunzura masu zanga-zanga a kansa.

ABNA: A cikin wani jawabinsa a daren jiya, Benjamin Netanyahu ya bayyana kafofin yada labaran Isra’ila da cewa mabarnata ne, suna gudanar da aiki ne da ke karfafa masu son rusa Isra’ila tare da boye gaskiya.

Netanyahu ya ce a duk lokacin da masu zanga-zanga suka kona wani gini na gwamnati ko suka rusa wata cibiya, to hakan laifin ‘yan jarida da kafofin yada labaran Isra’ila ne, domin su ne suke tunzura su.

Makonni 7 kenan a jere dubban yahudawa suna gudanar da zanga-zanga a cikin biranan Tel Aviv da Quds, suna kira ga Netanyahu da ya sauka daga kan kujerarsa, inda suke bayyana shi da mabarnaci mai cin hanci da rashawa.

A jiya ne aka gudanar da irin wannan zanga-zanga mafi girma da ke neman Netanyahu ya sauka, inda dubundubatar yahudawa suka halarta, kamar yadda kuma har a wasu garuruwan Amurka yahudawa sun gudanar da irin wannan zanga-zanga a jiya.

342/