ABNA: Shugaban na kasar Syria wanda ya gabatar da jawabi dangane da cika shekaru 75 da kafuwar sojojin kasar ta Syria ya kara da cewa; “ A kodayaushe sojojin Syria sun kasance a tare da al’ummar Syria a fagen fada da ‘yan ta’adda da hakan ya sa su ka sami gagarumar nasara.”
Shugaba Basshar Assad ya kuma bayyana cewa sojojin kasar ta Syria suna a matsayin abin alfahari, tare da jinjina musu, jami’ansu da kuratansu a wannan lokacin na bikin kafuwar sojan kasar.
Har ila yau, shugaban kasar ta Syria ya bukaci sojojin kasar da su ci gaba da nuna kwazo a fagen samun nasarori na tsaron kasa.
342/