ABNA24: sansanta rikicin siyasar kasar.
A wata sanarwa da wakilan masu zanga zangar, da ake wa lakabi da M5-RFP, suka fitar a cikin daren jiya, sun ce shawarwarin na ECOWAS, kwata-kwata basu daidai ba da bukatu da kuma abunda mafi yawan al’ummar kasar ta Mali ke jira gani ba.
Kafin hakan dai a jiya Asabar, jagoran tawagar ta ECOWAS, tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya bayyana wa ‘yan jarida cewa tattaunawar bata cutura ba, kuma tawagar za ta ci gaba da aikinta.
Daya daga cikin babban sabanin dake akwai shi ne na ci gaba da kasancewar shugaban kasar Ibrahim Bubakar Keita kan mulki, wanda kuma masu boren ke bukatar murabus dinsa.
Masu zanga zangar a kasar ta Mali, na zargin shugaban kasar da kasawa wajen shawo kan matsalolin da kasar ke fama dasu a sahun gama matsalar tsaro da kuma cin hanci da rashawa.
342/