16 Yuli 2020 - 13:59
Putin: Takunkuman Da Amurka Ta Dorawa Iran Ba Su Da Wani Amfani

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana cewa takunkuman tattalin arzikin da Amurka ta dorawa kasar Iran ba su da wani amfani, don ba za su taba kauda kasar kan abinda take a kai ba.

ABNA24: Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a tattaunawa ta wayar tarko da ta hada shi da shugabar gwamatin kasar Jamus Angela Merkel. Majiyar fadar Krimlin ta kara da cewa shuwagabannin biyu sun tattauna batutuwa da dama daga ciki har da batun kyautata dangantaka tsakanin kasashen biyu da kuma mutunta yarjejeniyar shirin nukliyar kasar Iran wacce aka fi sani da JCPOA.

Labarin ya kara da cewa yarjejeniyar shirin nukliyar kasar Iran wacce kudurin kwamitin tsaro na MDD na 2231 yake goyon bayan shi ne kadai hanyar tabbatar da zaman lafiya a yankin.

342/