12 Yuli 2020 - 12:44
Kamfanonin Magunguna Na BioNTech Da Pfizer Zasu Samar Da Alluran Riga Kafin Korona A Wannan Shekara

Manya-manyan kamfanonin samar da magunguna a duniya Pfizer da BioNTech sun bada sanarwan cewa zasu kammala marhalolin samar da riga kafin cutar Korona a karshen wannan shekara ta 2020.

(ABNA24.com) Jaridar world street Journal ta kasar Amuraka ta bada sanarwan cewa a halin yanzu riga kafin yana cikin marhala ta farko na gwaji a kan mutane, ana saran bayan samun izini a cikin wannan watan na Yuli da muke ciki, Pfizer da BioNTech zasu shiga marhala ta biyu ta gwajin riga kafin, wanda yake bukatan mutane dubu 30 wadanda zasu gabatar da kansu don gwajin.

Sai kuma bayan wannan marhalar kamfanonin zasu samar da kwalba miliyon 100 na alluran a karshen wannan shekara, sannan a shekara ta 2021 kuma za su samar da wasu kwalabe biliyon 1 da miliyon 200.

Cutar korona dai ta bulla a karon farko a birnin Wuhan na kasar Cana a karshen shekarar da ta gabata, amma a halin yanzu kusan ta game duniya gaba daya. Ya zuwa yanzun cutar ta kama mutane fiye da miliyon 12.5 sannan ta kashe fiye da rabin miliyon daga cikinsu..

342/