ABNA24: Shugaban kasar ta Iran ya ci gaba da cewa; Idan har ‘yan kasa su ka ci gaba da daukar cewa babu wata matsala komai ya dawo daidai, to za mu fuskanci matsala ta ci gaba da yaduwar cutar ta corona, idan kuma su ka dauka tsorata ta yadda za a dakatar da dukkanin hada-hadar tattalin arziki to shi ma akwai hatsari.
Shugaban kasar ta Iran ya yi ishara da wajabcin dakatar da yin taruka na bukukuwa ko zaman makoki saboda kaucewa kamuwa da cutar ta corona.
Har ila yau shugaba Dr. Hassan Rauhani ya bayyana cewa; Iran tana cikin kasashen da suke kokarin samar da riga-kafin cutar ta corona.
342/