5 Yuli 2020 - 12:03
​Libya: An Ragargaza Wasu Makaman Kariya Na Turkiya A Kusa Da Tripoli

Rahotanni daga kasar Libya na cewa, da jijjifin safiyar yau jiragen yakin dakarun Khalifa Haftar sun ragargaza wasu makaman kariya da Turkiya ta jibge a kusa da birnin Tripoli.

(ABNA24.com)  Tashar RT ta bayar da rahoton cewa, tashar Libya Hadas ta nakalto daga bangaren dakarun Haftar cewa, an kai harin ne a kan wasu makaman kariya da Turkiya ta jibge a cikin wani sansanin soja na Nafi’u Bin Uqba da ke wajen birnin Tripoli.

Rahoton ya ce, daga cikin abubuwan da ke wurin akwai na’urorin rada, da kuma na’urori masu harba makamai masu linzami da ke kakkabo jiragen yaki, wadanda dukkaninsu an ragargaza su.

Rahoton ya ce a ranar Alhamis da ta gabata ce Turkiya ta girke makaman, kuma a yau aka sanar da ministan tsaron kasar ta Turkiya wanda yanzu haka yana birnin Misrata na kasar Libya cewa, an kamma girke makama, kuma za su iya fara aiki a kowane lokaci.

Dakarun Haftar suka ce suna bibiyar dukkanin abin da yake faruwa, har zuwa lokacin da aka sanar da ministan tsaron an Turkiya, a kan haka ne suka kaddamar da hari a yau suka ragargaza dukkanin na’urorin da kuma makaman kariyar da Turkiya ta girke a wannan sansani.

342/