5 Yuli 2020 - 12:01
​Rauhani Ya Aike Wa Shugaban Aljeriya Sakon Taya Murnar Ranar Samun ‘Yancin Kasar

Shugaban kasar Iran Hassan Rauhani ya aike da sakon taya murna zuwa ga takwaransa na kasar Aljeriya Abdulmajid Tabun, kan zagayowar ranar samun ‘yancin kasar.

(ABNA24.com)  A cikin sakon nasa, shugaba Rauhani ya bayyana alaka tsakanin kasashen Iran da Aljeriya da cewa alaka ce ta tarihi, wadda kuma take bunkasa a kowane lokaci.

Dangane da zagayowar ranar da kasar Aljeriya ta fice daga karkashin mulkin mallaka kuwa, Shugaba Rauhani ya ce yana isar da sako na taya murna ga dukkanin al’ummar kasar Aljeriya, tare da yi wa kasar fatan samun ci gaba a dukkanin bangarori.

Tun shekaru 58 da suka gabata ne dai a rana irin ta yau wato 5 ga watan Yuli 1962, Kasar Aljeriya ta sami 'yancin kanta daga hannun turawan Faransa ‘yan mulkin mallaka.

Kafin haka turawan sun mamaye kasar Aljeriya ne a shekara ta 1930, kuma wannan halin ya ci gaba har tsawon shekaru 130.

Amma bayan yakin duniya na daya mutanen kasar Aljeriya sun fara wani sabon yunkuri na kwatar 'yancin kasar, inda aka kashe kimanin mutane miliyan daya, daga nan ne shugaban kasar Faransa na Lokacin Charles Digol ya baiwa mutanen kasar Aljeriya 'yancin kai a rana irin ta yau.

342/