25 Yuni 2020 - 07:23
​NLC Ta Koka A Kan Yawaitar Rasa Ayyuka A Nijeriya

Shugaban kungiyar kwadago ta NLC a Najeriya Ayuba Wabba, ya nuna damuwa matuka kan yadda ma’aikatan kasar da yawa suke ta rasa ayyukansu.

(ABNA24.com)  Jaridar Leadership ta bayar da rahoton cewa, Shugaban kungiyar kwadago ta NLC ya bayar da shawara ga masu daukar ma’aikatan da su daina hanzarin korar ma’aikatan nasu, a maimakon haka su ci gaba da tattalin ma’aikata bisa la’akari da abin da ke aukuwa a wasu sassan duniya.

Ayuba Wabba ya ce, Najeriya ba daya muke da wasu sassan duniya da suka ci gaba ba, kuma matsalar korar ma’aikata tana matukar yin barazana ga zaman lafiyar kasar.

Shugaban kungiyar ta NLC ya yi kira da a hau teburin tattaunawa a matsayin wata hanya ta hana korar ma’aikata daga bakin ayyukansu.

Ya ce babban aikin kungiyar kwadago shi ne samar da hanyar tattaunawa domin kare abin da ake samu, da kare barazanar rasa ayyuka.



/129