24 Yuni 2020 - 07:21
​Okonjo-Iweala Ce ‘Yar Takarar ECOWAS A Neman Shugabancin WTO

A cikin wata sanarwar da ta fitar kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta yamma Ecowas ta goyi bayan takarar Dr. Ngozi Okonjo-Iweala a matsayin shugabar kungiyar cinikayya ta duniya.

(ABNA24.com)  A cikin wata sanarwar da ta fitar kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta yamma Ecowas ta goyi bayan takarar Dr. Ngozi Okonjo-Iweala a matsayin shugabar kungiyar cinikayya ta duniya.

Rahotanni sun ce bayan da Najeriya ta mika sunan Okonjo-Iweala, dukkanin kasashe mambobi an kungiyar ECOWAS sun goyi bayan tsayawarta takarar neman kujerar shugabancin kungiyar cinikayya ta duniya.

Najeriya ta bayyana cewa ta mika sunan Okonjo-Iweala ne bisa la'akari da kwarewarta a fannin ilimi da kuma bangaren aiki kan abin da ya shafi tattalin arzikin Najeriya da zamanta ministar harkokin kudi a 2003 da kuma 2011.

Tun bayan da aka kafa kungiyar cinikayya ta duniya a shekara ta 1995, babu wani dan Afirka da ya taba zama shugaban kungiyar, wanda hakan ne yasa aka bude kofa domin bayar da sunayen mutanen da ake ganin sun dace daga nahiyar Afirka domin su shiga takarar kujerar shugabancin kungiyar.

Kasashen ECOWAS sun bukaci sauran kasashen Afirka da su mara wa Okonjo-Iweala baya domin samun wannan matsayi, kamar yadda kuma suka bukaci sauran kasashe da ba na Afirka ba, da su goyi bayan takarar ta Okonjo-Iweala .


/129