(ABNA24.com) Jaridar Premium times ta Najeriya ta nakalto majiyar ‘yansanda a jihar ta na tabbatar da labarin, sannan kakakin ‘yansanda a jihar Mohammad Shehu ya kara da cewa wannan ba shi ne karon farko da ‘yan bindiga suka kai hare-hare a kan wannan yankin ba.
A ranar 2 da kuma 3 ga watan yunin da ya gabata ma ‘yan bindigan sun kai farmaki a wannan yankin inda suka kashe mutane 2.
Wani wanda ya ganaewa idanunsa, wanda kuma baya son a bayyana sunansa ya fadawa wakilin jaridar Premium times kan cewa ‘yan bindiga kimani 200 ne haye a kan babura kimani 100, suka shigo garin da misalign karfe 6 na yamma.
Bayan shigowarsu suka fara bude wuta kan mai uwa da wabi, sannan suka sa ce dunikiyoyi da dabbobi masu yawa suka kora suka tafi da su.
Majiyar ta kara da cewa an kai wadanda suka ji rauni zuwa asbitin Dansadau inda wasu daga cikinsu suka rasa rayukansu a can.
/129