(ABNA24.com) Majalisar dokokin jamhuriyar musulinci ta Iran, ta yi allawadai da kakkausar murya da kudirin baya baya nan na majalisar gwamnonin hukumar yana yaduwar makamman nukiliya ta duniya (IAEA).
A wata sanarwa da majlaisar ta fitar mai dauke da sa hannun mambobinta 240 sun yi tir da abunda suka danganta da nuna wariya a hukumar.
Iran, ta bada misali da wani rahoton hukumar ta IAEA, dake cewa, a cikin shekaru shiga da suka gabata, damar data baiwa hukumar na gudnar da bincike ya karu daga kashi 4% zuwa 20% a Iran.
A wani share kuma Iran, ta gode wa kasashen da suka ki goyan bayan kudirin data danganta da abun kunya, da kuma matsin lamba daga abokan gabanta wanda a cewarta ba zai haifar da da mai ido ba.
/129
22 Yuni 2020 - 09:46
Lambar labari: 1049011
Majalisar dokokin jamhuriyar musulinci ta Iran, ta yi allawadai da kakkausar murya da kudirin baya baya nan na majalisar gwamnonin hukumar yana yaduwar makamman nukiliya ta duniya (IAEA).