(ABNA24.com) - A wata sanarwa da ta fitar, gwamnatin GNA, ta ce kalamai irin wandanda shugaban Masar, ya yi, tsoma baki ne a harkokin cikin gidan kasar, hasali ma tamakar shelanta yaki ne kan kasar Libiya.
Gwamnatin ta Tripoli, ta bukaci kasashen duniya, dasu sauke yaunin da rataya a wuyansu, kan abunda ta danganta da tada fitina, saidai kuma ta ce a shirye ta ke ta zauna tebirin tattaunawa a shiga tsakanin MDD.
Masar, dake goyan bayan Kahalifa Haftar, ta bakin shugaban kasar Abdel Fatah Al-sisi ta yi barazanar aike wa da sojoji a kasar ta Libiya, bisa da’awar cewa kutsen sojojin gwamnatin Tripoli, dake samun goyan bayan Turkiyya a birnin Syrte dake da matukar mahimanci a gabashin kasar tsallake jan-layi ne.
Cacar baki data barke tsakanin Masar da Libiya, na zuwa ne kwana biyu kafin taron kafar bidiyo na ministocin kungiyar kasashen Larabawa kan batun kasar ta Libiya, wanda gwamnatin Tripoli ta ki amince halarta.
A wannan Litini ce aka so gudanar da taron, saidai bayanai sun ce an dage shi har zuwa ranar Talata saboda matsalar na’urori.
Libiya ta fada cikin rikici ne tun bayan guguwar neman sauyin data yi awan gaba da mulkin tsohon shugaban kasar Mu’amar Ghadaffi a cikin shekara 2011.
/129
22 Yuni 2020 - 09:39
Lambar labari: 1049009
Gwamnatin hadin kan kasa a Libiya, dake samun goyan bayan MDD, ta yi tir, da abunda ta danganta da shelar yaki kanta, barazanar da kasar Masar ta yi na tura sojoji a kasar.