21 Yuni 2020 - 08:09
Rauhani: Za A Bude Makarantu A Ranar 5 Ga Watan Satumba

Shugaban kasar Iran Dr. Hassan Rauhani ya fada a yau Asabar cewa; sabuwar shekarar karatu ta bana za ta fara ne daga ranar biyar ga watan Satumba,bisa la’akari da matakan kiwon lifiya na fada da cutar corona.

(ABNA24.com) Shugaban kasar Iran Dr. Hassan Rauhani ya fada a yau Asabar cewa; sabuwar shekarar karatu ta bana za ta fara ne daga ranar biyar ga watan Satumba,bisa la’akari da matakan kiwon lifiya na fada da cutar corona.

Shugaban na kasar Iran ya kuma bayyana cewa; Da akwai bukatar a rika amfani da takunkumin rufe fuska a yayin shiga cikin jama’a.

Shuganan na kasar Iran ya kara da cewa; Daga nan zuwa kwanaki 123-na bude makaranta- da akwai bukatar al’ummar Iran, ma’aikatan kiwon lafiya, da dukkanin jami’an gwamnati su zage damtse wajen wayar da kai da ci gaba da daukar matakan fada da cutar ta corona.

Har ial yau, Dr. Hassan Rauhani ya ce; Saboda har yanzu babu allurar riga-kafin cutar ta Corona, kuma cutar ba ta sauya salon yadda take ba, wajibi ne mu kasance cikin shiri domin fada da ita na lokaci mai tsawo.

Bugu da kari shugaban na kasar Iran ya sake yin kira ga al’ummar kasar da su zama masu kula da bayar da tazara a yayin shiga cikin mutane, yana kuma mai kara da cewa a wasu yankunan sanya takunkumi zai zama dole.

Shugaba Dr. Hassan Rauhani ya ce yadda Iran ta yaki cutar corona ya fi na wasu kasashe da su ka ci gaba saboda hadin kai da ke tsakanin al’umma.


/129