20 Yuni 2020 - 09:47
Jordan : Mamayar Falasdinu, Zai Iya Hargitsa Gabas Ta Tsakiya

Kasar Jordan, ta bayyana shirin Isra’ila, na mamayar Falasdinu, a matsayin wata babbar barazana ga kokarin samar da zaman lafiya.

(ABNA24.com)  Da yake sanar da hakan yayin wata ziyarar ba-zata a Falasdinu, ministan harkokin wajen kasar Jordan, Ayman Safadi, ya ce shirin da Isra’ila ke yi na mamaye yankunan Falasdinawan, zai iya jefa yankin gabas ta tsakiya cikin wani rikici da ba’a san lokacin karewarsa ba, sannan zai kawo karshen duk wani kokari da ake na samar da kasashen biyu Isra’ila da Falasdinu.

A ranar 1 ga watan Yuli mai shirin kamawa ne Isra’ila za ta yi bayyani na aiwatar da shirin na mamayar yankunan yammacin kogin Jordan dake cikin tsarin nan na shugaba Trump da ya baiwa Israi’la damar mamaye Falastinu da kusan kashi daya cikin uku.

A watan da ya gabata dai kasar Jordan, wacce ita da Masar ne kawai kasashen Larabawa dake da hulda da Isra’ila, ta yi barazanar yanke huldar dake tsakaninta da yahudawan sahayoniya, idan Isra’ilar ta aiwatar da shirin na ta.

Dama kafin hakan sarkin sarkin Jordan, Abdallah II, ya nanata matsayin kasarsa na adawa da shirin na Isra’ila.




/129