(ABNA24.com) Wannan dai ya biyo bayan shafe shekaru hudu, ba’a samu wani mai cutar ba a kasar, dake yaki da cutar tun cikin 1988.
Gwamnatin Kamaru, ta bayyana matakin da babbar nassara, saidai ta ce hakan ba zai sanya ta yi watsi da matakan yaki da cutar ba, da suka hada da sanya ido da kuma yin shaushawa.
Baya ga Kamaru akwai kasashen da suka hada da Sudan ta Kudu, da Najeriya da kuma Jamhuriyar AFrika ta tsakiya, da suke neman shaidar rabuwa da cutar.
WHO ta ce takardu da kuma bayanan da kasashen na Afirka suka gabatar sun cika dukkan sharudan ayyana su a matsayin wadanda ba su da cutar polio, amma dai ana bukatar karin bitar yanayin da suke ciki kafin a bayar da sanarwa ta karshe kan matsayinsu game da cutar mai nakasa yara.
/129
20 Yuni 2020 - 09:14
Lambar labari: 1048218
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta amince cewa babu sauren cutar polio ko kuma shan-inna a Jamhuriyar Kamaru.