14 Yuni 2020 - 09:15
Iran:An Kama Alkalin Da Ake Zargi Da Cin Hanci Da Rashawa A Kasar Romania

Majiyar ma’aikatar shari’a ta kasar Iran ta bada sanarwan cewa wani alkalin kasar wanda ake zargin da karban cin hanci na Euro 500,000 a kasar, an kama shi a kasar Romania.

(ABNA24.com) Majiyar ma’aikatar shari’a ta kasar Iran ta bada sanarwan cewa wani alkalin kasar wanda ake zargin da karban cin hanci na Euro 500,000 a kasar, an kama shi a kasar Romania.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin ma’aikatar shari’a Gholam-Hossein Esmaeili yana fadar haka . Ya kuma kara da cewa an kama tsohon alkalin mai suna Gholamreza Mansouri, tare da taimakon ‘yan sandan kasa da kasa wato “Intapol”, kuma zasu ci gaba da tsare shi har zuwa lokacinda aka samu dama dawo da shi gida don fuskantar sharia.

Kakakin ma’aikatar shari’ar ya ce a halin yanzu babu girgin da zai dawo da shi gida saboda matsalar cutar Corona wacce ta dakatar da zirga-zirgan jiragen sama a kasashen duniya. Ana zargin Gholamreza Mansouri ne a shari’ar da akewa tsohon mataimakin alkalin alkalan kasar Akbar Tabari na cin hanci da rashawa.

Alkalin alkalan kasar ta Iran Hujjatul Islam Ra’esi ya kuduri anniyar binciken jami’an ma’aikatar shari’ar dangane da zargin da ake masu na yada fasadi a ma’aikatar a cikin shekarun da suka gabata.


/129