8 Yuni 2020 - 06:12
An Sake Zargin Sojoji Da Kisan Fararen Hula A Mali

Rahotanni daga Mali, na cewa fararen hula 29 ne aka kashe a kauyen Binedama dake yankin Koro a tsakiyar kasar.

(ABNA24.com) Rahotanni daga Mali, na cewa fararen hula 29 ne aka kashe a kauyen Binedama dake yankin Koro a tsakiyar kasar.

Bayanai daga kasar sun ce wasu mutane ne sanye da kakin soji sukayi kawanya wa kauyen.

Ganau sun ce mutanen sun zo yankin ne cikin motoci kimanin arba’in.

Kungiyar Fulani ta Tabital Pulaaku, ta ce an kashe fararen hula 29, tare da zargin sojojin kasar da aikata kisan.

Tuni dai ma’aikatar tsaron kasar ta Mali, ta sanar da gudanar da bincike kan lamarin.


/129