(ABNA24.com) - Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gargadi ‘yan bindiga da suka addabi jihar Katsina da su mika kansu da makamansu ga jami’an tsaro, ko kuma su kuka da kansu.
Mai taimaka ma shugaba Buhari a bangaren hulda da manema labarai Garba Shehu ne ya fitar da sanarwar wadda ke cewa; shugaba Buhari ya jajanta wa al’ummar jihar Katsina dangane da hare-haren da ‘yan bindiga suke kaddamarwa a wasu yankuna na jihar.
A cikin makon da ya gabata ne dai ‘yan bindiga suka kashe hakimin ‘Yantumaki a jihar ta Katsina, kamar yadda kuma suka kashe shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Batsari.
Buhari ya yi gargadin cewa ba za a sassauta wa ‘yan bindiga da suke aikata irin wannan ta’asa ba, matukar dai ba su mika kansu da makaman da ke hannunsu ba.
Yanzu haka dai an tura daruruwan sojoji da jami’an tsaro zuwa yankunan da ‘yan bindigar suka addaba a cikin dazukan Batsari na jihar Katsina, kamar yadda kuma shugaba Buhari ya yi alkawarin cewa za a kara karfafa tsaro a cikin yankunan da ‘yan bindigar suka addaba a sauran jihohi, musamman Katsina, Kaduna, Zamfara, Neja da kuma Sokoto.
/129
7 Yuni 2020 - 09:24
Lambar labari: 1044143
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gargadi ‘yan bindiga da suka addabi jihar Katsina da su mika kansu da makamansu ga jami’an tsaro, ko kuma su kuka da kansu.