(ABNA24.com) A Mali daruruwan ‘yan kasar ne suka gudanar da wata zanga zanga ta nema ga shugaban kasar Ibrahim Boubakar Keita ya yi murabus.
An gudanar da zanga zangar ce bisa kiran wasu kungiyoyin fara hula na kasar da jam’iyyun adawa na kasar.
Bangarorin na zargin shugaban kasar da kasawa wajen shawo kan matsalar tsaro dake addabar kasar.
Masu zanga zangar sun baiwa shugaban kasar wa’adin mako guda na ya yi musu bayyani ko kuma su sake fitowa a mako mai zuwa.
/129
6 Yuni 2020 - 05:43
Lambar labari: 1043644
A Mali daruruwan ‘yan kasar ne suka gudanar da wata zanga zanga ta nema ga shugaban kasar Ibrahim Boubakar Keita ya yi murabus.