(ABNA24.com) Majalisar Dinkin Duniya, ta yada da cafke Félicien Kabuga, daya daga cikin attajiran da ake zargi da taimakawa kisan kiyashin Rwanda.
A ranar Asabar data gabata ne dai ‘yan sanda Faransa suka cafke M. Félicien Kabuga, daya daga cikin jiga-jigan mutanen da ake tuhuma da hannu wajen assasa kisan kare dangin da aka yi a Rwanda cikin shekarar 1994.
Babbar kwamishinar hukumar kare hakin bil adama ta MDD, Michelle Bachelet, ta ce hakika cafke M. Kabuga, zai taimaka sosai wajen zakulo sauren mutane bakwai dake da hannu a kisan kiyashin Rwanda.
Jami’ar ta ce, tana fatan hakan zai sanya dukkan kasashen su rubanya kokarinsu da kuma matakan da suka wajaba domin gano sauren mutanen domin su ma su gurfana gaban shari’a.
/129
20 Mayu 2020 - 07:34
Lambar labari: 1038615
Majalisar Dinkin Duniya, ta yada da cafke Félicien Kabuga, daya daga cikin attajiran da ake zargi da taimakawa kisan kiyashin Rwanda.