18 Mayu 2020 - 04:31
Isra’ila : An Gano Jakadan China Mace A Gidansa

Rahotanni daga Isra’ila na cewa an gano jakadan kasar China, mace a gidansa dake arewacin birnin Tel Aviv.

(ABNA24.com) Rahotanni daga Isra’ila na cewa an gano jakadan kasar China, mace a gidansa dake arewacin birnin Tel Aviv.

Bayanai sun ce an gano jakadan ne, mace a cikin gadonsa da sanyin safiyar yau Lahadi.

Du Wei, dan shekaru 57 ans, an nada shi jakadan kasar China a Isra’ila a ranar 15 ga watan Fabarairu, bayan kammala aiki a Ukraine.

Babu dai tabas akan musababin mutuwar tasa, saidai bayanai sun ce ya killace kansa na tsawon makwanni biyu, bayan ya gana da wasu jami’an Isra’ila da suka kamu da cutar korona.



/129