(ABNA24.com) Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto firai ministan sanye da rigar dakarun na PMU yana cewa rundunar abin alfakhiri ne ga kasar Iraqi.
Alkazimi ya je cibiyar dakarun PMU ne a dai-dai lokacinda tashar talabijin ta kasar Saudiya MBC ta watsi wani shirin wanda ya ci mutuncin shaheed Mahdi Almuhandis shugaban dakarun wanda sojojin Amurka suka kashe tare da Janaral Qasim Sulaimani a farkon wannan shekara a birnin Bagadaza.
An kafa dakarun PMU ne a shekara 2014 bayan bullar kungiyar Daesh a kasar Iraqi, tare da fatawar Ayatullahi Sayyeed Assistani babban malamin addini a kasar.
Sai kuma a shekara 2016, bayan ta sami nasara kan kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh, gwamnatin kasar Iraqi ta sanya dakarun cinkin jirin jami’an tsaron kasar Iraqi.
Kungiyar ta taka rawar a zo a gani wajen yakar kungiyoyin ‘yan ta’adda a kasar Iraqi musamman kungiyar Deash.
A ziyar dai Alkazimi ya gana da shugaban dakarun na PMU Falih al-Fayyadh, inda ya tabbatar masa goyon bayansa ga rundunar.
/129
17 Mayu 2020 - 08:00
Lambar labari: 1037604
Sabon firai ministan kasar Iraqi Mustafa Alkazimi ya ziyarci cibiyar dakarun hasdushaabi (PMU) a jiya Asabar a birnin Bagdaza.