16 Mayu 2020 - 06:26
An Bukaci A Dau Matakan Gaggawa Na Rage Cunkoson Fursunoni A Nijeriya

Alƙalin alƙalan Nijeriya Mai shari’a Tanko Muhammad ya buƙaci alƙalan aƙalan jihohin ƙasar da su ɗau matakan gaggawa wajen ganin an rage cunkoson fursunoni a gidajen yarin ƙasar sakamakon ci gaba da yaɗuwar annobar coronavirus.

(ABNA24.com) Alƙalin alƙalan Nijeriya Mai shari’a Tanko Muhammad ya buƙaci alƙalan aƙalan jihohin ƙasar da su ɗau matakan gaggawa wajen ganin an rage cunkoson fursunoni a gidajen yarin ƙasar sakamakon ci gaba da yaɗuwar annobar coronavirus.

Mai shari’a Tanko Muhammad ya bayyana hakan ne cikin wata wasiƙa da ya aike wa alƙalan alƙalan jihohin a yau Juma’a 15 ga watan Mayu inda ya ce a halin fursunonin da suke tsare a gidajen yari daban-daban na ƙasar sun kai mutane 74,127 wanda 52,226 suna jiran shari’a, inda ya ce a mafiya yawan wajajen da ake tsare da mutane suna tsare da mutanen da yawansu ya ninninka yawan adadin mutanen da ya kamata a ce ana tsare da su a wajen ne, wanda hakan barazana ce ga yanayin lafiya.

Alƙalin alƙalan na Nijeriya ya ci gaba da cewa a saboda haka akwai bukatar a ɗau matakan gaggawa wajen rage adadin waɗanda ake tsare da su ɗin musamman idan aka yi la’akari da halin da ake ciki na yaɗuwar annobar COVID-19, don haka ya buƙaci alƙalan alƙalan jihohin da su fara wani rangadi zuwa gidajen yarin da suke ƙarƙashinsu wajen ganin an sake fursunonin da suka cancanci a sake su don rage cunkuson.

A kwanakin baya ma dai shugaban Nijeriyan Muhammadu Buhari ya ba da umurnin sake wasu fursunoni da suka cika sharuɗɗan afuwan da shugaban yayi musu don rage cunkuson da kuma barazanar ci gaba da yaɗuwar annobar Coronavirus ɗin.


/129