(ABNA24.com) Kasuwar sararin samaniya a Afirka na ci gaba da bunkasa, inda aka kiyasta cewa Nahiyar na samar da dala biliyan 7 a duk shekara , wanda acikin shekaru 20 an kaddamar da Tauraron dan Adam guda 32 a kasahen Afrika guda 8, inda 3 daga cikinsu wasu hukumomin a nahiyar Afirka ne suka dauke nauyi,
Yanzu haka dai nahihar Afrika na ci gaba da bunkasa a bangaren kera Tauraron dan Adam , inda a halin yanzu kasar Tunusiya ta samar da tauraron dan Adama na farko da aka yi shi a cikin gida mai suna Kalubale,
Kamfanin TELNET na kasar Tunusiya ne ya samar da shi tare da taimakon kasar Rasha, kuma ana saran za’a harba shi a ranar 15 ga watan Nuwamba mai zuwa, kashi 100 % na kayayyakin da aka yi amfani dasu na cikin gida ne,
Akwai hanyoyi da dama da za’a yi amfani da tauraron dan Adam din da ya hada da samar da wutar lantarki ta hasken rana a yankunan sahara da kuma bibiyan dabbobin da ke kiwo a iyakar kasar da kuma kasashen Algeria da Libiya dake makwabtaka da ita.
/129
14 Mayu 2020 - 04:30
Lambar labari: 1036700
Kasuwar sararin samaniya a Afirka na ci gaba da bunkasa, inda aka kiyasta cewa Nahiyar na samar da dala biliyan 7 a duk shekara , wanda acikin shekaru 20 an kaddamar da Tauraron dan Adam guda 32 a kasahen Afrika guda 8, inda 3 daga cikinsu wasu hukumomin a nahiyar Afirka ne suka dauke nauyi,