(ABNA24.com) Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya musanta cewa gwamnatinsa na da hannu a kokarin kutsawa cikin kasar Venezuela a ranar Lahadin da ta gabata wanda wasu ‘yan ta’adda suka yi.
Kafin haka ma ma’aikatar harkokin wajen Amurka da kuma Pentagon duk sun musunta cewa Amurka tana da hannu a cikin wanann lamari.
‘Yan ta’addan dauke da makamai sun gamu da turjiya daga sojojin kasar Venezuela wadanda suka kashe 8 daga cikinsu sannan suka kama mutane 13 da ransu.
A wani jawabin da ya yi wa mutanen kasar bayan wannan yunkurin, shugaban kasar ta Venezuela Nicolas Maduro ya ce ‘yan ta’addan, daga ciki har da Amurkawa biyu, sun kuduri aniyar kashe shi da kuma wasu daga cikin jami’an gwamnatin kasar.
Rahoton ya kara da cewa ‘yan ta’addan sun fito ne daga kasar Colomba inda suka sami horon soji, sannan Amurkawa biyu da aka kama, masu suna Airan Berry da Luke Denman su na dauke Passport na Amurka, da wasu takardun shaida da suka nuna cewa suna aiki da wani kamfanin tsaro mai suna Silvercorp USA a jihar Florida ta Amurka.
Tun farko shekara ta 2019 ne shugaban Amurka ya kuduri anaiyar kifar da gwamnatin Nicolas Maduro, domin ya maye gurbinsa da John Guaido abokin hamayyarsa a matsayin shugaban kasa.
/129
7 Mayu 2020 - 04:38
Lambar labari: 1034345
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya musanta cewa gwamnatinsa na da hannu a kokarin kutsawa cikin kasar Venezuela a ranar Lahadin da ta gabata wanda wasu ‘yan ta’adda suka yi.