7 Mayu 2020 - 04:38
Fitaccen Masani A Turkiya Ya Rasu Saboda Kamuwa Da Corona

Omar Dogel Auglo fitaccen masani marubuci dan kasar Turkiya ya rasu sakamakon kamuwa da cutar corona.

(ABNA24.com) Kamfanin dillancin labaran anatoli ya bayar da rahoton cewa, a jiya ne Omar Dogel Auglo fitaccen masani marubuci dan kasar Turkiya ya rasu sakamakon kamuwa da cutar corona a asibitin Pashak da ke kasar Turkiya yana da shekaru 52.

Ya shahara a kasar Turkiya a bangaren rubuce-rubucensa da kuma bayanan da yake gabatarwa  a bangaren tarihin muslunci da kuma tarihin rayuwar manzon Allah.

Ya kasance daga cikin masu kaunar ahlul bait (AS) da kuma yada koyarwarsu a tsakanin al’ummar musulmi a kasar Turkiya, ta hanyar gidajen talabijin musammana  cikin watan Ramadan.

Rajab Tayyib Erdogan shugaban kasar Turkiya ya aike da sakon ta’aziyya, tare da bayyana rasuwarsa a matsayin wani babban rashi ga dukkanin al’ummar kasar.


/129